
A zaman wata babbar kotun jihar Kano dake zaune a Bompai a ƙarƙashin mai Shari’a Justice Nasiru Saminu kuwa, kotu ce ta wanke wata mata ƴar garin Takai da ake zargi da kashe kishiyarta subul da sabulu.
Kotun dai ta sallami Hajara Abubakar ne da ake zargi da kashe kishiyarta.

A zaman kotun na yau, mai shari’ar ya sallami wacce ake tuhuma ne biyo bayan gaza kawo wanda ake zargin su tare.
Da yake bayani, lauyan da ke kare ta, Barrister Shazali Muhammad, ya roƙi kotu da cewar, tunda lauyoyin gwamnati sun gaza, yana roƙon kotu data sallami shari’ar. Haka akayi kuwa.
Bayan fitowa daga kotun ne, Jaridar Mikiya ta zanta da lauyan da yake kareta. A saurare shi:
“Lokutan da aka bawa shi lauyan gwamnati ya gabatar dasu tare, bai gabatar dasu ba har kusan wata ashirin, don haka ita wanann kotu mai adalci ta duba cewar, yaya wadancan suna can suna yawon su, suna shakatawa ita kuma tana tsare.
“Ba’ada bayan haka, kotu tayi la’akari da rashin lafiyar ta, domin tana da rashin lafiya ta Diabetis”.

Haka ita ma matar data shaƙi iskar ƴancin, tayiwa jaridar Mikiya bayani:
“Gaskiya ni bazan taɓa kwatanta irin wannan farin ciki ba, tunda nake a rayuwa ta ban taba jin irin wannan farin ciki ba, sai ranar da aka ce an bada beli na, na tafi gida.
Ba kuma abinda zance da kotu sai dai godiya”.
Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru