Sheikh Dr Pantami ya rage kudin Data da Kashi 50%

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis tace an rage kudin ‘Data’ da kashi 50% bisa umurnin da aka baiwa hukumar sadarwan Najeriya NCC. Saboda haka, kudin ‘Data’ na 1GB ya sauko daga N1000 zuwa N487 daga yanzu (watan Nuwamba). ‘Data’ kudi ne da mutum ke saya a domin amfani da samun shiga yanar gizo. Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, wanda ya sanar da hakan ya ce, an yi hakan ne bisa umurnin da aka baiwa hukumar NCC na tabbatar da cewa an rage kudin ‘data’ a fadin tarayya.
Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage kudin ‘Data’ da kashi hamsin (50%), Pantami ya sanar a Facebook

madogara Legit Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published.