Shekaru 4 Kenan Ana Titin Abuja Zuwa Kano a Amma Har Yanzu Ko Kilomita 10 Ba’a Kammala Ba, Inji Buba Galadima

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Tsohon na hannun damar shugaba kasa, Muhammadu Buhari, Buba Galadima ya sake caccakar gwamnatin shugaban kasar kan cewa a bayyane take cewa ta gaza.

A hirar da yayi da gidan talabijin na Channelstv wanda wakilin hutudole ya bibiya, Buba Galadima ya bayyana cewa duk abinda Gwamnatin APC ta fada babu wanda ta cika.

Yace sun ce zasu yashe kogin Naija amma basu yi komi ba, sun yi Alkawarin Titi da sauran ayyukan raya kasa, Misali titin Abuja zuwa Kano shekaru 4 kenan ana yinsa amma har yanzu ko Kilomita 10 ba’a yi ba.

Buba ya bayyana cewa yayi tafiya daga Abuja zuwa Gashua kuma ya sha wahala.

Leave a Reply

Your email address will not be published.