Shin Dr Pantami yasan Katin Dan Kasa da layin waya an Fara na Bogi a Nageriya?

Yanzun nan muka rabu da wani bawan Allah ya kawo sabuwar wayar da ya saya domin in yi masa back-up na contacts daga gmail nasa.

Ina tambayarsa ko ya yi linking na NIN (lambar katin ɗan kasa) da Simcard nasa? Ya ke amsa mun da cewa ai bayada National ID card. Na ke faɗamashi cewa ai kuwa ina ganin za a dakatar da duk layin da ba’a haɗa shi da NIN ba nan da wani ɗan lokaci.

Shin ne yake bani labari ai a unguwarsu idan baka da Katin ɗan kasa akwai masu yi maka linking na layinka da nasu katin, sai ka bayar da N500, kafin in gama mamakin hakan ya cigaba da bani labarin cewa ai yanzu ma idan kana da katin ɗan kasa zaka iya kaiwa sai a baka dubu uku, sai su ɗauki katin hoton lambar NIN ɗin, sai su cigaba da karɓar ɗari biyar biyar suna yiwa mutane linking, har sun gano NIN ɗaya tana yiwa mutane 20.

Da farko abin ya bani dariya to amma hatsarin da ke ciki yasa na dakatar da dariyar.

Da farko dai an fitar da wannan aiki ne domin sauƙaƙawa jami’an tsaro wajen bankaɗo duk wani layi da aka yi amfani da shi wajen aikata ɓarna ko laifi, ta hanyar amfani da kundin ajiyar bayanai na katin ɗan kasa, wanda yake tattare da bayanai masu yawa na mai ɗauke da katin.

To yau mun wayi gari saboda, talauci ko son abin duniya, ko jahiltar hatsarin da ke ciki, zaka bayar da katinka na ɗan kasa a baka N2,000 alhali baka san wanda za a haɗa layinsa ba da lambar katinka. Nan gaba duk aika aikar da ya aikata kana zaune gida baka ci baka sha ba azo a naɗe ka.

Wannan ya nuna akwai buƙatar wayar da kan jama’a game da hatsarin da ke cikin wannan.

Muna kira ga hukumomin da wannan aiki ya shafa da gidajen radio da television musamman na gwamnati da su taimaka wajen wayar da kan jama’a akan wannan ɗanyan aiki da suke neman ɗebowa kansu

Allah ya kyauta madogararmu a Wannan labari Mohammed Garba MG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *