Shugaba Buhari ya taya Aminu Ɗantata murnar cika shekaru 90 a duniya

SHUGABA BUHARI YA YABA WA AMINU DANTATA MAI SHEKARU 90, YA BAYYANA SHI A MATSAYIN BABBAN DAN KASUWA ABIN KOYI.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya murna ga mashahurin ɗan kasuwan Kano, Alhaji Aminu Ɗantata, bisa bikin zagayowar ranar haihuwarsa shekara 90, a ranar 19 ga watan Mayun shekaran 2021.

A cikin sako zuwa gare shi Shugaba Buhari yace:

“Tarihin iyalan Ɗantata abun ishara ne kuma mai kyau. iyali da tun farko suke nan, amma sun canza sun saka kansu cikin kasuwanci sun yi nasara ta hanyar aiki tukuru, hangen nesa da kuma kafiya.

“Bada ka taba tafiya ta hanyan tarihi na Dantata ba tare da ka kasance ka yaba daga kasuwanci na ruhu da ta yadda suka gina harsashen mahaifin su daga karfi zuwa karfi.”

Shugaban kasa ya yaba wa Aminu Dantata bisa gudanarwan sa na fasaha da kuma gudanar da kasuwanci a matsayin aiki zuwa ga al’umma ta hanyan aikin taimako.

Daga Mutawakkilu Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *