Shugaba Buhari ya yi abin kirkin da babu wani shugaba daya taɓa yi a tarihin Najeriya- Inji Lai Mohammed

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Abin Kirki Sama Dana Kowanne Shugaba A Tarihin Najeriya

Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Mohammed ya yi alfaharin akan babu shugaban Najeriyar daya taɓa yin abubuwan alheri a tarihin ƙasar sama da wannan gwamnatin ta Muhammadu Buhari tun bayan data samu madafin iko a shekarar 2015.

Ministan ya yi wannan maganar ne a loƙacin daya ke tattaunawa da kafafen watsa labaru dangane da cikar gwamnatin shugaba Buhari shekaru shida akan karagar mulkin Najeriya, ya bayyana cewa gwamnati ba zata yi ƙasa a gwiwa ba wajan yin amfani da kafafen watsa labaru domin nuna abubuwan alherin data aiwatar a lungu da saƙo na cikin ƙasar wanda hakan zai shiga cikin kundin tarihin ƙasar sannan ya kunyatar da waɗanda su ke sukar gwamnati akan babu wani abin a zo a ganin data yi a cikin waɗannan shekarun data kwashe tana mulki

Ya ƙara cewa “Abu ne mafi sauƙi a mu mance, amma idan za a tuna wannan gwamnati ta zo ne a daidai loƙacin da farashin ɗanyen man fetur ya faɗi warwas a kasuwannin duniya wanda shine ya ke samar da kaso 80 daga cikin kuɗaɗen da ake kasafin kuɗi a ƙasar sannan ya ke samar da kaso 90 na musayar kuɗaɗen ƙetare”.

Dan haka a bayyane ya ke, nasarorin da wannan gwamnatin ta cimma suna da matuƙar yawa duk da ƙarancin kuɗaɗen data fuskanta.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *