Buhari ya cika shakara 6 akan mulki haryanzu Babu nasara a sashin tsaro.

A yau Asabar 29 ga watan Mayu 2021 Shugaba Muhammadu Buhari yake cika shekara shida tun bayan da ya karɓi mulki daga hannun tsohon Shugaba Goodluck Ebele Jonathan a shekarar 2015.

Nasarar ta Shugaba Buhari ta tabbata ne biyo bayan irin goyon baya da miliyoyin ƴan Nigeria suka bashi na tabbatar da cewa yayi nasara musamman a zaɓen farko wanda ya gudana a watan Maris ɗin shekarar 2015.

Hakan kuma ya faru ne bayan gazawar da tsohon Shugaba Goodluck Ebele Jonathan yayi na magance matsalar tsaro musamman a Arewa maso gabashin ƙasar, cin hanci da rashawa tare da rashin samun damar aiki musamman ga miliyoyin ƴan ƙasar da suka kammala karatu a wancan loƙacin; wanda waɗannan sune kaɗan daga cikin dalilan da ya sanya mutanen Nigeria suka buƙaci Shugaba Buhari da ya Shugabanci ƙasar domin a tunaninsu da zarar ya shiga ofis, waɗannan matsaloli sun kau.

Abin mamakin shine, shekaru kaɗan bayan Shugaba Buhari ya kama aiki a matsayin Shugaban ƙasar ta Nigeria, sai gashi ɗaukacin al’ummar ƙasar suna kokawa da irin salon mulkin na sa, yayinda waɗansu suke iƙirarin cewa al’ummar Nigeria sun fi samun sauƙi da arahar rayuwa a loƙacin da Tsohon Shugaba Goodluck Ebele Jonathan yake Shugabantar ƙasar.

A loƙacin yaƙin neman zaɓensa na farko a shekarar 2015, Shugaba Buhari dai yayi alƙawura a wurare daban-daban waɗanda har kawo yanzu babu alamun an ɗauko hanyar cika su.

Duk da rashin cika waɗannan
alƙawura; abin mamaki sai gashi Shugaba Buharin ya sake lashe zaɓe a karo na biyu wanda ya gudana a shekarar 2019, bayan da wasu ƴan Nigeria suke ganin cewa ya dace a ƙara bashi dama domin tabbatar da gyaruwar al’amura a faɗin Nigeria.

Abun takaici sai gashi yau abubuwa sai ƙara lalacewa suke; duba da yadda matsalar tsaro take ƙara ta’azzara a Nigeria, matsin tattalin arziƙi, bazuwar cin-hanci da rashawa tare da tsadar rayuwa da ba’a taɓa ganin irinta a faɗin ƙasar ta Nigeria ba.

Cikin ikon Allah yau kuma shekara biyu ya ragewa Shugaba Buhari ya sauka daga karagar mulki. Shin ko akwai wani ƙwarin gwiwa da ya ragewa mutumin Nigeria a yanzu?

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *