Shugaban karamar hukumar kunbotso a Kano ya nada masu bashi shawara mutun Hamisin da biyar 55.

Shugaban karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano, Hassan Garban Kauye Farawa, ya nada masu ba da shawara na musamman da mataimaka guda 55.

Yayin da yake rantsar da su a ofis, Farawa ya ce nadin nasu ya yi daidai da manufar Gwamna Abdullahi Ganduje na kawar da talauci.

Ya bukaci sabbin nade-naden da su sauke nauyin da ke wuyansu tare da kwazo don ciyar da karamar hukumar gaba.

“Nadin mataimakan na 55 sakamakon kokarin da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi, na kawar da talauci a tsakanin matasa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar kano musamman a wannan mawuyacin lokaci,” in ji shi.

Shugaban kungiyar ya yi kira ga wadanda aka nada su zama jakadu na kwarai tare da kaucewa duk wani abin da zai bata sunan karamar hukumar Kumbutso da jihar Kano.

Kansilan Ward na Gurungawa na Karamar Hukumar Kumbotso a kwanan nan ya nada masu taimaka masa 18, lamarin da ya haifar da tashin hankali.

Aminiya ta ruwaito cewa kansilan ya ce ya ba da gudummawar albashinsa na farko ne domin karfafawa mutane 100 da ke fama da nakasa a shiyyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *