Labarai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani asusun bada tallafi na N62bn domin taimakawa Najeriya kawo karshen cutar kanjamau.

A yau, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani asusun bada tallafi na N62bn domin taimakawa Najeriya kawo karshen cutar kanjamau.
Cutar ƙanjamau (HIV) ta kasance barazana ga lafiyar al’umma, haka kuma ana samun karin masu dauke da cutar kanjamau a duk shekara.
A wajen kaddamar da shirin, Shugaban kasa Muhammadu ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da fifiko kan harkokin kiwon lafiya don magance cututtuka masu saurin kisa.