Sojoji sun kashe ‘yan bindiga uku yayin da su Kuma ‘yan Bindigar Suka Kashe mutun biyu a venue.

Sojojin Operation Whirl Stroke (OPWS) sun kashe wasu mutane uku da ake zargin ‘yan fashi ne a wata musayar wuta da suka yi a daren Lahadi a garin Adaka da ke karamar Hukumar Makurdi a Jihar Benuwai.

Daily trust ta gano daga wasu mazauna yankin cewa ’yan bindigar sun yi wa Adaka kawanya, wani yanki da ke kusa da garin Makurdi kuma suna zargin suna yi wa mazauna yankin fashin lokacin da sojoji suka kawo musu dauki.
An sanar da cewa sojojin sun samu kiran gaggawa daga mazauna garin yayin da suke sintiri a kusa da yankin kuma a kokarin fatattakar ‘yan bindigar, sai aka yi artabu da yan bindigar yayin da aka kashe mutanen uku.
Mazauna yankin sun fadawa manema labarai a Makurdi cewa lamarin wanda ya faru da misalin karfe 8 na dare zai iya zama mafi muni amma saboda saurin kai dauki da sojoji suka yi saboda ‘yan fashin sun riga sun harbi wani mutum da matarsa.

Lokacin da aka tuntubi Kwamandan rundunar ta OPWS, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya tabbatar wa manema labarai cewa tawagar sintirin ta yi arangama da wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai a yankin na Adaka.

“Sojojinmu kuma za su yi duk mai yiwuwa tare da sauran jami’an tsaro a kasa don kare jama’a,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.