Sunaye sun bayyana na ‘yan Najeriya da aka kama da laifin turawa ‘yan ta’addan Boko Haram kudi

Ta fasu: Sunayen ‘yan canji a Najeriya da aka kama suna turawa ‘yan Boko Haram kudi

– Sunaye sun bayyana na ‘yan Najeriya da aka kama da laifin turawa ‘yan ta’addan Boko Haram kudi


– Da yawa daga cikinsu ‘yan canji ne da masu siyar da gwal dake budaddiyar kasuwar Wapa a Kano

– Daga cikinsu akwai Baba Usaini, Abubakar Yellow (Amfani), Yusuf Ali Yusuf (Babangida), Ibrahim Shani, da sauransu

A watan da ya gabata ne Malam Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa akan yada labarai, yace gwamnatin tarayya ta kama wasu ‘yan canji da ke turawa ‘yan Boko Haram kudi.

Ya ce wasu ‘yan Najeriya dake zama a daular larabawa (UAE) sune ke aiki da ‘yan canjin wurin turawa ‘yan ta’addan kudi.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *