Talaka Kada Ya Damu Da Karin Farashin Man Fetur Saboda Shi Ba Mota Ko Janareto Gareshi Ba – Cewar Garba Shehu.

Garba Shehu ya bayyana cewa mazauna birane ke amfana da man fetur ba na karkara ba

A cewarsa, karin farashin ba zai shafi talakawa ba saboda basu da kayan alatun dake bukatar mani

Fadar shugaban kasa bata gushe ba tana kare karin farashin man fetur, yayinda mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya kara jaddada muhimmancin hauhawar.

Garba Shehu ya ce yawancin yan Najeriya basu amfani da man fetur saboda haka ba zasu amfana da rashin tsadarta ba, hakazalika tashin farashin ba zai shafesu ba.

Gwamnatin Buhari a farko shekarar nan ta bayyana shirinta na cire tallafin mai tare da sauye-sauye a bangaren mai.

Tun daga lokaci farashin ya dan sauka bisa ga saukar farashin danyar mai a kasuwan duniya sakamakon bullar cutar Korona.

Amma a watan Satumba, farashin ya fara hauhawa kuma hakan ya tayarwa yan Najeriya hankali.

Wasu sun daurawa gwamnatin laifin bari farashin ya tashi duk da cewa yan najeriya na fama da tasirin annobar Korona a rayuwarsu.

A ranar Juma’a. yayinda hira a shirin Politics Today a tashar ChannelsTV, mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, ya ce babu adalci ace talakawa su cigaba da baiwa mazauna birni tallafi.

“Shin yan Najeriya nawa suka mallaki mota? Yan Najeriya nawa ke amfani da Janareto a giidajensu da suke bukatar mai? Shin akwai adalci manoni da makiyayi da talakawa, a rika daukan kudinsu ana biyan tallafin mai ga mazauna birni?” Shehu ya ce

“Saboda haka shugaban kasa na kokarin fito da komai fili ne kan lamarin.”

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published.