Tambuwal na wani Shirin wargaza Jam’iyar PDP domin niyyarsa ta tsayawa takara a 2023 ~Inji Lere

Wani Babban Jigo a jam’iyyar PDP daga jihar kaduna(Alhaji Adamu musa lere) yana zargin Gwamnan Sokoto Rt Hon. Aminu waziri Tambuwal da kunno rikici a jam’iyyar PDP dake arewa maso yammacin kasar nan don kare muradinsa na tsayawa takara a zabe mai kara towa (2023).

Wannan yama zuwa ne a dai dai lokacin da jam’iyyar ke shirin zaben shugabanninta na shi’ar arewa maso yamma(Northwest) wanda aka cinma matsaya a taron masu ruwa da tsaki, inda aka baiwa kowacce jiha mukaminta. Taron zai gudana ne a jihar kaduna ranar asabar 10-04-2021. Jihar kano tana da kujeru kamar haka; (National northwest vice chairman, National Woman leader zonal, Ex officio national da zonal).

Sai dai Dan siyasar yana zargin gwamna tambuwal da hambarar da wancan yarjejeniya da uwar jam’iyya tayi inda tuni aka samu labarin ya siyi Tikiti na mataimakin shugaba(National Northwest vice chairman) don bawa wani makusanci kuma jigo a jam’iyyar PDP a jihar kano.

Wannan yunkuri ne da gwamnan yakeyi domin kawo rudani da rikici a cikkn jam’iyya PDP a jihar kano dama shiyar ta gaba daya.

Alh lere yayi kira ga uwar jam’iyya da tayi gaggawar bincikar wannan al’amari fa kuma daukan mataki domin gujewa abinda ka iya jefa jam’iyyar ga rashin nasara kamar yanda yafaru a zaben daya gabata.

A cewarsa, jihar kano itace cibiyar siyasa a arewacin Najeria kuma jihai mai yawan kuri’u, wanda yin hakan na iya jefa Jam’iyyar cikin rudani a zabe mai gabato wa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *