Tarihin rayuwar Sanata Aisha Jummai Alhassan

Takaitaccen Tarihin Marigayiya Hajiya Aisha Jummai Alhassan (Mama Taraba)

An haife ta ranar 16 ga watan Satumbar shekarar 1959 a garin Jalingo na jihar Taraba.

Ta kammala jami’ar ABU Zaria a shekarar 1985, ta zama Sanata mai wakiltar arewacin jihar Taraba daga shekarar 2011 zuwa 2015 a karkashin Jam’iyar PDP.

Ta tsaya takarar gwamnan jihar Taraba a shekarar 2015 a karkashin inuwar Jam’iyar APC, bayan tayi rashin nasara shugaba Buhari ya bata ministar mata sai dai tayi murabus a shekarar 2018 bayan wani rikici da ya kunno kai saboda nuna goyon bayanta ga Atiku Abubakar wanda hakan ya yi sanadiyar ficewarta daga Jam’iyar APC zuwa Jam’iyar UDP.

Ta rasu ranar Juma’a 7 ga watan Mayu, 2021, Tanada Shekaru 61 a Duniya.

Allah Ubangiji Ya Yi Mata Rahama.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *