Tinubu ya raba tulin buhunan kayan abinci domin Musulmai su samu abin buda-baki

Sama da mutum 4, 000 su ka amfana da kayan shan ruwan da babban jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tibubu, ya raba a jihar Katsina.

Jaridar Katsina Post ta rahoto cewa Bola Ahmed Tibubu ya taimaka wa marayu da kuma masu karamin karfi da abin da za su yi buda-baki a Katsina.

Shugaban kwamitin rabon wannan kaya, Alhaji Salisu Mamman, ya shaida wa manema labarai wannan a lokacin da yake gabatar da wadannan kayan.

Kamar yadda Salisu Mamman ya bayyana, kayan abincin da aka raba sun hada da kilo biyar na shinkafa.

Salisu Mamman ya tabbatar da cewa bayan marayu da marasa hali, za a raba kayan abincin ga yankunan da ‘yan bindiga su ka yi ta’adi a jihar Katsina.

Mamman wanda ya ke da alhakin raba kayan shan ruwan, ya ce Bola Tinubu ya yi wannan abin alheri ne domin Bayin Allah su samu abin yin buda-baki.

Wannan abin alheri ya zo ne a daidai lokacin da aka shiga kwanaki goma na karshen watan Ramadan, an fara hango shirye-shiryen bikin karamar idi.

Da yake jawabi, Alhaji Salisu Mamman, ya sha alwashin cewa zai yi adalci da gaskiya wajen raba wa wadanda su ka cancanta wadannan kayan karya azumi.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *