Labarai

TIR’KASHI: Bayan shekaru 37 a Kurkuku, an saki mutumi bayan an gano karya akayi masa

Spread the love

Wani mutumi a kasar Amurka ya samu yanci bayan shekaru 37 a kurkuku yayinda aka gano karyar laifin kisan kai akayi masa a shekarar 1984 a birnin Philadelphia.

Mutumin mai suna, Willie Stokes, wanda aka saki a watan Junairu 2022 ya shigar gwamnatin kotu kan zaluncin da aka masa.

Associated Press ta ruwaito cewa mutumin da ya bada shaida a kotu a kansa a 1984 ya bayyana cewa kwayoyi da yan mata akayi masa alkawari ya yiwa Willie Stokes sharri.

Willie Stokes yace: “Komai ya wuce. Ina farin ciki zan cigaba da rayuwata.”

Sama da mutane 100 aka saki kawo yanzu a jihar Pennsylvania dake Amurka bayan sun kwashe shekaru a kurkuku, Diraktan ceto masu gaskiya a jihar Pennsylvania, Marissa Boyers Bluestine, ta bayyana.

Mutumin da yayi shaida shekaru 37 da suka gabata mai suna Franklin Lee, yace daga baya ya yi nadamar sharrin da yayi masa. Sai Lauyoyin gwamnati suka hukuntashi kan karya da sharri kuma shima aka jefashi kurkuku.

A baya mun kawo cewa an saki wani mutumi mai suna Kevin Strickland a kasar Amurka da ya kwashe shekaru 43 cikin gidan yari kan laifin da ba shi ya aikata ba.

Kevin Strickland wanda dan garin Missouri ne a Amurka, ya shaki kamshin yanci ranar Talata, 23 ga Nuwamba, 2021. Alkali James Welsh ya wanke mutumin daga laifukan da ake zarginsa da su na kisan mutum uku.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button