Tsagerun IPOB sun kone ofishin ‘yan sanda, sun sheke jami’ai 2 a Anambra

Kasa da sa’o’i 24 da nada sabon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Anambra, Christopher Adetokumbo Owolabi, ‘yan bindiga sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda dake Obosi a karamar hukumar Idemili a jihar inda suka sheke ‘yan sanda biyu.

‘Yan bindigan sun kai farmaki ofishin ‘yan sandan a yammacin Laraba inda suka saki dukkan masu laifi dake ofishin sannan suka banka masa wuta, Daily Trust ta wallafa.

Majiyar tace wadanda abun ya shafa aka kashe su ne a wani gidan mai kusa da ofishin ‘yan sandan.

Majiyar tace yayin da ‘yan sandan ke kan aikinsu, sun gane cewa akwai ‘yan bindiga dake kaiwa da kawowa, lamarin da yasa suka fara gudu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra ya tabbatar da kisan jami’an har biyu.

DSP Tochukwu Ikenga, kakakin rundunar ‘yan sandan, wanda ya tabbatar da harin, yace kwamishinan ‘yan sandan jihar ya tura jami’ai domin duba yadda lamarin yake.

Ikenga ya kara da cewa an mika gawawwakin ‘yan sandan ma’adanar gawawwaki kuma ana cigaba da bincike.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *