Tsagin Aminu Wali na cigaba da shan bakar wahala a hannun Kwankwaso

Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta musanta rahotannin dake yawo a kafafen watsa labarai na cewa jam’iyyar ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda tace wasu dai-daikun mutane ne masu burin haddasa fitina ne suka shirya wancan zance mara tushe.

Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, PDP ta bakin sakataren watsa labaranta na kasa, Kola Ologbondiyan, ta bayyana cewa ba zata lamunci makamancin wannan shashanci daga wasu dai-daikun mutane marasa biyya ba, wadanda suka bar hanyar shiriya suka koma ta bata, domin kawo rashin jituwa a jam’iyyar, da kuma rage mata daraja a idon al’umma.

Haka zalika jam’iyyar ta PDP ta musanta rahoton cewa ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Niger, Dr. Babangida Aliyu, sannan ta roki jagororin jam’iyyar na jihar Kano da Niger, da dukkan magoya bayanta dasu lura sosai, su cigaba da aiki don samun mafutar Nigeria a hannun PDP, cikin yanayi mara dadi da ake ciki a yanzu.

A jiya ne dai jam’iyyar PDP ta jihar Kano, tsagin Ambasada Aminu Wali, da sanar da dakatar da Kwankwaso da dukkan magoya bayansa daga jam’iyyar, tare da bawa Kwankwaso wa’adin awanni 48 don ya bayyana a gabanta bisa amsa korafin da aka shigar akansa, kan yadda magoya bayansa suka yayyaga takardu da tada hargitsi yayin zaben shugabannin jam’iyyar na Arewa maso yamma, ranar 10 ga wata a jihar Kaduna, bisa umarnin shi Kwankwaso.

Daga: Kano Online News
18/04/2021

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *