TUNA BAYA: Bola Tinubu da Gwamnan Oyo ne suke daukar nauyi tare da bawa kungiyar OPC makamai domin kashe hauwasa a Jihar Lagos ~Cewar Sheikh Ja’afar Mahmood Adam.

A wani tsohon sautin murya an ji muryar Sheikh Ja’afar Mahmood Adam Mai rasuwa Yana magana akan yadda wasu Shugabannin yarabawa suka daurewa ‘yan Kungiyar OPC gindin domin kashe hausawa ‘yan arewa nazauna kudancin Nageriya musamman jihar Lagos da Oyo.

Sheikh Ja’afar a cikin jerin sunayen da ya lissafo wanda yace jininsu ya halatta Tsohon Gwamnan jihar Lagos Bola Ahmad Tinubu shine mutun wanda yazo na bakwai inda Sheikh Ja’afar Yace Bola Tinubu ya kira Taron sulhu na zaman lafiya a lokacin da ake tsaka da kashe hausawa a taron an kira Sarkin Inyamurai Sarkin Hausawa Shugabannin tsaron ‘yan Sanda Dana Soja da Kuma Shugaban kungiyar OPC wacce shehun malamin Yace kungiyar Ce ke daukar nauyin ta’addancin kashe kashe da ake a lagos a wancan lokacin amma Bola Tinubu ya ki taka masu burki.

Sheikh Ja’afar Yace a taron da aka gudanar domin zaman lafiya Shugaban kungiyar OPC ya fice daga Taron Kuma Sam Yaki aminta daya Saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a lokacin tare Kuma haka Bola Tinubu ya kyaleshi ya fita.

Bincike ya nuna cewa Gwamnan Oyo da Bola Ahmad Tinubu na daga cikin wa’yanda ke daukar nauyin kungiyar tare da Basu makamai inji Sheikh Ja’afar Mahmood Adam.

Tsohon Gwamnan jihar Lagos Bola Tinubu wanda ya kasance Dan takarar Neman shugaban kasa na jam’iyar APC yanzu haka Yana fuskantar barazana tare da turjiya gami da mummunar Adawa daga jama’ar arewacin nageriya.

One thought on “TUNA BAYA: Bola Tinubu da Gwamnan Oyo ne suke daukar nauyi tare da bawa kungiyar OPC makamai domin kashe hauwasa a Jihar Lagos ~Cewar Sheikh Ja’afar Mahmood Adam.

  • June 16, 2022 at 5:15 pm
    Permalink

    Mudai munatare da hamza almustafa

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *