Labarai

Wani dan sanda ya harbe wata lauya har lahira a ranar Kirsimeti a Legas

Spread the love

An kama wani mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) dake ofishin ‘yan sanda na Ajah da ke Legas, bisa zargin harbe wata Lauya mai suna Bolanle Raheem, har lahira a ranar Lahadi, yayin da take komawa gida tare da ‘yan uwanta daga wajen bikin Kirsimeti.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce an kama dan sandan da ya kashe ta ne bayan da shi da tawagarsa suka gudu daga wurin bayan harbin.

“Jami’in da ya yi harbin ASP ne; an kama shi, an tsare shi, kuma za a mika shi zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar, Panti, don ci gaba da bincike,” in ji Hundeyin.

Wani ganau da ya ga lamarin ya shaida wa manema labarai cewa marigayiyar, ‘yar uwarta, da ‘ya’yanta hudu suna fitowa daga gidan abinci a cikin motarsu da misalin karfe 11 na safe, sai dan sandan ya yi kokarin hana su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button