Wani mafarauci ya kashe wani dan fulani mai kiwo a cikin daji a jahar Ondo 

Wani mafarauci mai suna Seyi Sansere ya halbe wani dan fulani mai suna Muhammad Maikudi a cikin daji a kauyen Ifira ta karamar hukumar Akoko a jahar Ondo.

An samu labari cewa Seyi ya kashe Maikudi ne a yayin da yake kiwon shanun sa a cikin dajin.

Bala Umar, Shugaban al’ummar Hausa/fulani na jahar ne ya tabbatar da wannan lamarin.

Umar ya ce bincike ya nuna cewar wanda ya kashe wannan makiwaci ya bishi ne har cikin daji inda ya halbe shi.

Amma dai, yayi kirari ga fulanin da ke zama a wannan wuri da su kwantad da hankali kada suce zasu dauki mataki da kansu inda ya kara da cewa yan sanda suna kai ga lamarin kuma sun tabbatar da cewa za ayi adalci akan wannan lamari.

Kwamanda na kungiyar sojojin corps na Amotekun, Adetunji Adeleye yace “mafaraucin gida ne ya halbe wannan dan bafullatanin, babu ruwan ma’aikatan mu. Mu muna kokarin muga an samar da zaman lafiya a cikin al’umma”.

Mamacin wanda yazo daga jahar Katsina ya rasu ya bar ‘ya’ya biyu.

Daga Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *