Wasu ma’aikata sun tare hanya a fusace, sun hana tawagar motocin mataimakin gwamnan jihar Nasarawa wucewa saboda dalilin kin biyan su albashi da akayi. 

Ma’aikata a karamar hukumar Doma ta jihar nasarawa sun hada zanga zangar rashin biyan albashi har na wata biyu da kuma zargin bacewar miliyan ashirin wanda federal mortgage scheme (FMC) ta cire daga albashin su.

Ma’aikatan sun tare hanya a inda suka hana tawagar motocin mataimakin gwamna, Dakta Emmanuel Akabe, wanda shima daga karamar hukumar Doman yake.

Akabe, tare da council chiaman, Mr Rabi Sani, sun taru suna mai bawa wadannan mutane shawara da hakuri na su kwantad da hankulan su.

Sun tabbatar wa ma’aikatan cewa gwamnatin jihar tana kan kokarin ganin yadda zatayi domin taga an gyara wannan al’amari amma wadan nan ma’aikata sunki su saurare su hasalima, sai suka kashe hanyar wucewa.

Wannan rufe hanya da akayi an fara shi ne tun ranar litinin na wannan satin kuma a nan tsakiyar hanyar suka gudanar da “Addua’a ta musamman”.

Council chiaman din ya dora wa wadanda suka maye gurbinsa laifi na gazawar su wurin biyan ma’aikata albashi, inda yace daukar ma’aikata ba a kan doka ba shi ya janyo wannan matsala.
Ya fada cewa “Ban dauki ma’aikaci ko guda aiki ba amma wadanda suka maye gurbi na sunyi kuskure wurin daukar ma’aikata fiye da dari biyar”

Sannan kuma ya karyata maganar kudin da suka bata a inda yace “Kudin ba bata sukayi ba, amma an are su domin biyan ma’aikata albashi, sannan kuma ya kara da cewa gabadaya shuwagabannin yuniyan suna sane da wannan”

Ya kara da cewa kananan hukumomi guda goma sha uku na majalissar sun bukaci adadin kudi biliyan biyu domin biyan ma’aikata albashin wata biyu.

Maryam Gidado Yar’adua

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *