Labarai

Wata Budurwa lauya ‘yar shekaru Ashirin da tara 29 kenan da ‘yan bindiga Suka kashe ta a harin ta’addancin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna.

Spread the love

Wata Lauya budurwa ‘yar shekara 29 mai suna Farida Sule Mohammed, na daga cikin wadanda aka kashe a harin da ‘yan ta’adda suka kai kan jirgin kasa kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin 28 ga watan Maris.

Marigayiyyar wanda aka ce diya ce ga Sakataren Tsare-tsare na jam’iyar PRP na kasa, Mallam Sule Mohammed, Kamar yadda Dan uwanta ya tabbatar da rasuwarta shafinsa na Twitter.

An yi jana’izar ta a masallacin Yahaya Road da ke Kaduna da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Talata 29 ga watan Maris bayan kammala sallar jana’iza.

Wata kawarta Mai suna Zahida Barau ta bayyana marigayiya Farida a matsayin mutuniyar kirki mai kyakkyawar zuciya.

Tana Mai cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, jiya mun rasa Farida a harin jirgin kaduna _Abuja, tabbas na aminta yanzu ta samu wuri mafi kyau, mutuniyar kirki ce mai kyakkyawar zuciya, Halinki nagari ya biki Farida. Allah ka isar mana . jinin marar laifi ba zai taba tafiya a banza ba. Don Allah a yi wa kawata addu’a” inji ta Zahida.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button