Wata mata ta haifi ƴan tara a ƙasar Morocco

Kyauta Daga Allah: Wata Mata Ta Haifi Ƴan Tara a Morocco

Wata mata yar kasar Mali mai suna Halima Cisse yar shekara 25 ta haifi yan tara a kasar Morocco – Ministan Lafiya na Mali, Fanta Siby ta ce likitocin da suka raka Cisse Morocco sun tabbatar mata da hakan – Siby ta mika sakon taya murna ga likitocin Mali da Morocco bisa nasarar da suka samu na tiyatar haihuwan Wata mata yar kasar Mali ta haifi yan tara a Morocco a ranar Talata kuma dukkan jariran tara ‘lafiyarsu kalau’, a cewar gwamnatin kasarta duk da cewa mahukunta a Morocco ba su tabbatar da hakan ba, The Punch ta ruwaito. Gwamnatin kasar Mali ta kai Halima Cisse mai shekaru 25 daga yankin arewacin kasar zuwa Morocco domin samun ingantaccen kulawa a ranar 30 ga watan Maris. Da farko ana tunanin yan bakwai za ta haifa.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *