Labarai

Wata Sabuwa: CBN bai tuntubi ma’aikatar kudi kan sake fasalin kudin Naira ba – Zainab Ahmed

Spread the love

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, a ranar Juma’a ta ce babban bankin Najeriya bai tuntubi ma’aikatarta ba kafin ya yanke shawarar sake fasalin kudin Naira nan da Disamba.

Ta bayyana hakan ne a yayin muhawarar kasafin kudi na ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa a Abuja.

Ministar ta ce duk da cewa daya daga cikin dalilan da suka sa aka yanke wannan shawarar shi ne yadda za a shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, to tabbas sakamakon zai biyo baya.

“Ba a tuntube mu ba,” in ji ta. “Sanarwa ce muka ji. Wani bangare na dalilan da aka ba da shawarar shi ne cewa yana daya daga cikin hanyoyin da za a bi don magance hauhawar farashin kayayyaki.

“Amma akwai kuma sakamakon – muna duban yadda sakamakon zai kasance. Za a sami wasu fa’idodi amma za a sami wasu ƙalubale.

“Kuma ban sani ba ko hukumomin hada-hadar kudi sun yi nazari sosai kan menene sakamakon da kuma yadda za su rage shi.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button