Shahararren malamin addinin kirista na Adoration Ministry da ke jihar Enugu, Rev. Fr. Ejike Mbaka, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa, ya daina siyan jiragen yaki ya dukufa wajen gina karin masana’antu.
A cewar malamin na addinin kirista, sakon da ya fada wa Buhari daga ubangiji ne, PM News ta ruwaito.
Ya shaida wa shugaban cewa jiragen da yake sayowa za a yi amfani da su ne wajen lalata kasar.
Mbaka ya bayyana hakan ne a lokacin da yake wa’azi a cocin sa ranar Lahadi 10 ga watan Oktoba.
A kalamansa:
“Jiragen da kake saya za a yi amfani da su don durkusar da Najeriya.
“Don Allah, duk mutumin da ya fara saduwa da Shugaba Buhari bayan wannan sakon, ya gaya masa cewa duk wadannan jiragen da yake sayowa za a yi amfani da su don lalata Najeriya.
“Ubangiji ya ce in gaya masa haka.”
“Ya kamata ya daina siyan karin jiragen sama na yaki ya kuma fara gina karin masana’antu.”
Buhari, yayin da yake magana a makon da ya gabata, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta karbi karin kayayyakin aiki a ci gaba da ake da yaki da abokan gaba na kusa da na nesa.
A cewar Buhari:
“Za a tura wadannan kayan aikin don hanzarta yaki da rashin tsaro a dukkan sassan kasar.”
Daga Ahmad Aminu Kado.