Ya rasu a kan hanyarsa ta dawowa da wurin bude tafsirin dayakeyi a duk shekara.

-Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel

“Malam umar takensa shine JAN GAUSI, Ya rasu Sanadiyyar hatsari a mota, a bisa hanyarsa na dawowa daga wurin bude tafsirin Alquur’ani mai girma da yakeyi a duk shekara ga daya ga watan Ramadana.

Rahotonni sun shaidamana cewa! Bayan hatsarin da yayi, ya samu karaya masu rauni a jikinsa, inda ya danyi fama da jinya, daga karshe dai yace ga garinku nan.

Malamine mai hazaka, ga hidimtawa musamman akan harkan annabi muhammadu, ga kuma ilimin tsagwaran a kansa Wanda Allah ya hore masa, ya rasu ya bar matarsa guda daya tare da ‘ya’ya biyu.

Anyi jana’izarsa a yau Asabar 17-04-2021 cikin unguwansu mai suna rimin kambari cikin garin zariya jihar Kaduna.”

Allah yajikansa da rahama Amin.

Ahmad Aminu Kado….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *