Labarai

‘Ya ‘yan ku ba za su sake biyan ku’din WAEC da NECO da JAMB ba idan na zama shugaban Kasar Nageriya ~Cewar Kwankwaso.

Spread the love

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi alkawarin biyan kudin WAEC, NECO da JAMB na daliban idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zabe mai zuwa.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya ce idan aka zabe shi, sakamakon JAMB zai kasance shekaru hudu ne maimakon daya.

Ya ce, “Mun saurari korafe-korafen mutane, duk inda muka je, muna bayyana ma’anar mu da tsare-tsaren mu ga mutane musamman a fannin ilimi. Za mu gina aji a makarantun firamare 500,000 nan da shekaru hudu.

“Za mu yi rajistar daukacin yaran miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta, muna da shirin biyan WAEC, NECO ciki har da JAMB na dalibai kuma lokacin tabbatar da sakamakon JAMB zai kai shekaru hudu ba wai duk shekara dalibai suna zaune mata idan ba su samu ba. admission.”

Dangane da kawancen da suka yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Kwankwaso ya ce ya ki janye wa Peter Obi ne saboda ya fi shi kwarewa.

“Shi (Peter Obi) ya yi gwamna ne kawai amma na yi ayyuka daban-daban; Na yi aikin gwamnati na tsawon shekaru 17, bai yi ba, na zama mataimakin kakakin majalisar wakilai, bai yi ba. Na shiga taron tsarin mulki, bai yi ba.

Baya ga wadannan, ni Sanata ne, bai yi ba, Hatta iliminmu, idan ka duba, za ka gane cewa ba daya ba ne,” inji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button