Labarai

Ya zama wajibi Sojojin Nageriya su kasance na kowa da kowa a Lokacin zaben 2023 ~Cewar Shugaba Buhari.

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin Najeriya da su kasance na kowa kuma aiki domin kokarin ganin an samu nasarar zaben 2023 a kasar.

Ya ba da umarnin ne a lokacin da yake bayyana buda taron shekara-shekara na Hafsan Sojoji na 2022 da aka gudanar a Sokoto mai taken, “Gina Kwararren Sojan Najeriya don Muhalli na Tsaro na Karni na 21,” a ranar Litinin.

Shugaban ya ce ya zama wajibi rundunar soji ta tallafa wa hukumomin farar hula ta hanyar samar da yanayi na lumana don samun nasarar gudanar da ayyukanta.

Ya bayyana jin dadinsa yadda shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya riga ya fitar da wata doka da aka duba da kuma ka’idojin da’a don jagorantar ma’aikata yayin babban zaben.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button