Yadda gobara ta lamushe rayuka a Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce aƙalla mutane biyu ne ƴan gida ɗaya suka ruga mu gidan gaskiya a daren juma’a yayin da gobara ta tashi yankin gidan Zoo, wato daura da gidan kallon dabbobin da ke Kano, a can Sheka.

Alhaji Saminu Abdullahi, shine jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ya tabbatar da faruwar hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Asabar a Kano.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:10 na dare, a wani bene mai dauke da bangarori biyu mai kusan kafa 50 X 50 wanda aka yi amfani da shi a matsayin gida.

”Gobarar ta lalata dakuna sun huɗu, palour biyu, bandakuna biyu da kuma dakin dafa abinci guda biyu.

“Mun samu kiran waya daga Sabo Wada da misalin karfe 10:10 na dare cewa gobara tana cin wani gida a yankin yayin da wasu mutane uku suka shiga cikin tarko ciki har da yarinya‘ yar shekaru huɗu.

“Da samun wannan bayanin, sai muka hanzarta tura jami’anmu na ceto zuwa wurin da misalin karfe 10:15 na dare.

“An ceto mutum biyu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su a sume kuma an kai su asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano inda likita da ke bakin aiki ya tabbatar da cewa sun mutu.

”An mika gawarwakin ga C.S.P Awaisu Suleiman na reshen‘ ƴan sanda na Sheka,” in ji shi.

Sanarwar ta ce waɗanda lamarin ya rutsa da su sun hada da Fatima Salisu, 4, da Salisu Sani, mai shekaru 45, yayin da mutum biyun da suka mutu su ne Maryam Sani, ‘yar shekaru 19, da kuma Nafisa Abdulkarim, 28 (matar aure).

Sanarwar ta ce dukkan wadanda lamarin ya rutsa da su ‘yan gida daya ne kuma ana ci gaba da binciken musabbabin faruwar lamarin.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *