Yadda Sanata Uba Sani Ya Kashema ‘yan gudun Hijira Milyan Tamanin 80millions


Biyo bayan bullar hare-haren ta’addancin ‘yan bindiga a garuruwa Goma Sha bakwai 17 dake Karamar Hukumar Igabin ta jihar Kaduna Jama’ar kauyenku masu dimbin yawa ne suka tsere daga Gidajen su sukayi Gudun ceton ransu zuwa Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira A Makarantun Firamari  dake garin Birnin Yero,

mutanen ‘yan gudun neman ceton sun hada da ‘yan kauyakun Dallatu, Digani, Unguwar Audu, Bakin Kawsuwa, Jura, Unguwan Tofa, Sauran Giwa, Kosau, Kajinjiri da Kuma makeri,

  bayan faruwar Hakan ne gidauniyar ta Sanata Uba sani Wato UBA SANI FOUNDATION Cikin gaggawa ba tare da Bata lokaci ba ta Kai dauki ga ‘yan gudun hijirar ta hanyar taimakon su da kayan abinci kala kala domin Samun sauki harzuwa lokacin da Suka koma gida Bayan rikicin ya lafa…
Har’ila yau A yunkurin sa na taimakon al’ummarsa,  Cikin karamin lokaci Gidauniyar Uba Sani ta mamaye ko’ina a jihar ta kaduna wanda kawo yanzu ta Taimakawa talakawa marasa karfi masu tarin yawa a lokacin da suke tsaka da bukatar neman taimako, Kimanin Naira Miliyan tamanin 80Millions  gidauniyar ta kashe domin sayen kayayyakin taimakon Al’umma tun bayan barkewar Annobar Cutar Coronavirus.
Sanata uba sanin dai yace zamansa a Majalisar Dattijan Nageriya zai bashi damar taimakon Al’ummar Arewa a bisa baiwa da damar da Allah ya bashi, ya kuma tabbatar da cewa zai tsaya tsayin daka domin cigaba da taimako tare da tabbatar da wakilci na gari ga al’ummarsa ta jihar kaduna dama arewa baki daya…

Leave a Reply

Your email address will not be published.