Labarai

Yakamata Ko wacce Gwamnatin jiha ta kirkiro da Hukumar tattalin arzikin fasahar zamani ~Cewar Minista Pantami.

Spread the love

Ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital, Farfesa Alli Isa Pantami, ya bukaci gwamnatocin jihohi da su samar da ma’aikatar tattalin arziki ta zamani domin bunkasa tattalin arziki.

Pantami ya bayyana haka ne a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a jiya, yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Seyi Makinde, domin nuna jin dadinsa kan matakin da ya dauka na karbar bakuncin taron majalisar kan harkokin sadarwa da tattalin arziki na zamani karo na 10 da ke gudana a Ibadan.

Ministan, wanda ya karbi bakuncinsa a dakin taro na majalisar zartarwa na ofishin gwamna, Sakatariya, Agodi, Ibadan, ya yaba wa Gwamna Makinde bisa goyon bayan da ya bayar ga zaman da kuma karfafawa jihar gwiwa don kafa ma’aikatar tattalin arziki na dijital.

Ya tabbatar da cewa tattalin arzikin na’ura ya taimaka matuka wajen habaka tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma karuwar kudaden shiga na tarayya fiye da kowane bangare kuma bai Kamata a bar shi a karkashin wata ma’aikatar ba.

Ministan wanda ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya za ta aiwatar da muhimman manufofi daga takardar da aka gabatar bayan kammala taron karo na 10, ya bayyana cewa an zabi Oyo ne domin a ci gaba da al’adar shimfida hazaka a kowane shiyyoyin kasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button