Labarai

Yakamata mata su kulla alaka da ‘yan majalisa domin tabbatar da dokar Jinsi ~Cewar Sanata Uba sani.

Spread the love

Ranar mata ta duniya Sanata Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattijan Nageriya sanata Malam Uba sani ya jinjinawa daukakin matan duniya Sanatan ya bayyana wannan Sako ne a shafinsa na Twitter jiya talata ranar mata Sanata Yace matan duniya ina gaishe ku. Ina jinjinawa ƙarfin hali da juriya Duk da tarin kalubale da rashin daidaito da ke tattare da ku amma kun tsaya kan hanya wacce ta dace.

Yau ce ranar ku. Muna taya ku murnar zagayowar ranar mata ta duniya. wannan wata alama ce kunshe da tunatarwa ga masu tsara manufofi a duniya cewa suna bukatar su rubanya kokarinsu don tabbatar da daidaiton jinsi.

Matan Najeriya sun kasance a sahun gaba wajen fafutukar tabbatar da daidaito tsakanin jinsi da adalci. Sun nuna jarumta domin samun damammaki da dama a fagen siyasa da tattalin arziki. Sun kasance suna ba da gudummawa sosai ga ci gaban tattalin arzikinmu da siyasa. Don haka matanmu sun cancanci goyon baya da Bayar da kwarin guiwa domin shiga sahun gaba gaba ba tare da nuna bambanci ko hanawa ga harkokin mulki da al’amuran jama’a ba. Ya kamata tsarin manufofinmu ya rinka hadawa dasu domin Nemo masu basira da kwazo su duk domin ci gaban kasarmu nageriya.

Sanatan ya Kara da cewa Ina kira ga matan Najeriya da su dau matakin kulla alaka da mazaje domin a gaggauta amincewa da dokar yaki da wariya da jinsi a Majalisar Dokoki ta kasa. Dole ne a bayyana batutuwan ga maza ‘yan majalisa kuma a kawar da fargabarsu. Dole ne a kawar da tsarin hadin gwiwa tare da aiwatar da shi domin tabbatar da daidaita jinsi a tsara manufofi da tafiyar da harkokin mulki a Najeriya. domin Najeriya ta samu ci gaba mai dorewa, dole ne a baiwa mata dama daidai gwargwado.

Barkanku da Ranar Mata ta Duniya

Sanata Uba Sani,
Kaduna Central Senatorial District

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button