Yakamata ‘yan Nageriya su San ma’anar Sabuwar Rundunar SWAT.

Sufeto janar na ‘yan sanda, Mohammed a ranar Lahadi ya rusa rundunar‘ yan sanda ta musamman da ke yaki da fashi da makami kuma a ranar Talata, ya sanar da cewa, Runduna ta SWAT zata maye gurbin SARS. akwai wasu abubuwan da ya kamata ku sani game da Rundunar:

  1. Jami’an SWAT zasu tunkari kararrakin fashi da makami da sauran laifukan ta’addanci.
  2. Masu yuwuwar daukar matakin SWAT zasu fara horo a cibiyoyin horar da dabarun ‘yan sanda daban-daban a duk fadin kasar, mako mai zuwa.
  3. Wadanda zasu zama membobin zasu yi gwajin lafiyar jiki da kwakwalwa
  4. Za’a gudanar da gwajin lafiyar ne ta hanyar sabon sashin kula da bada shawara da tallafawa ‘yan sanda (PCSU).
  5. Tsoffin jami’an SARS ba za su taba kasancewa cikin sabuwar Rundunar SWAT ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.