Rahotanni daga iyakokin Nageriya ya nuna Cewa Masu fataucin kayan abinci daga Arewa zuwa kudancin Najeriya sun fara komawa fidda kayan abinci zuwa makobtan kasashe.
Kamar yadda kuke gani, nan shine iyakar Najeriya ta jihar Sokoto, waɗannan mototi makare da abinci sun nufi birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, wasu kuma Abidjan na kasar Cote d Ivoir, yayinda wasu kuma zasu birnin Accra na kasar Ghana, domin cinikayya.
Wannan lamari na zuwa ne biyo bayan katse huldar cinikayya da masu saida kayan abincin sukayi da yankin kudancin Najeriya.