Yan Arewa San Kanku Yayi Yawa, “Inji Dattawan Inyamurai”

Daya daga cikin dattawan Inyamurai, Cheif Mbazulike Amechi ya bayyana cewa, mutanen Arewa sun cika son kansu da yawa.

Yana martanine akan matsayar kungiyoyin kare Muradun Arewa na cewa, suna goyon a canja fasalin kasa amma ba su fitar da matsaya akan tsarin mulkin karba-karba ba.

Yace a bisa doka, Shugaban kasar Najeriya na iya fitowa daga kowace jiha. Yace amma a 2023 idan manya jam’iyyun Siyasa basu tsayar da Inyamuri takarar Shugaban kasa ba, to shine da kanshi zai jagoranci kauracewa babban zaben.

Yace mulkin sojoji da aka yi a Najeriya ne ya lalata kasar, wanda kuma duka ‘yan Arewa ne suka yishi in banda Janar Obasanjo, yace shima da Murtala bai mutu ba, da bai yi mulkin ba.

Yace kuma sune suka raba Najeriya zuwa jihohi daban-daban inda suka nuna son kawo ta hanyar baiwa Arewa jihohi 19 fiye da kudu.

Daga Comr Haidar Hasheem Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *