‘Yan bindiga a kan babura sun shiga garin Kore dake Dambatta, Sun dunga ruwan wuta babu sassauci

Bayan luguden ruwan wutar da suka yi a daren Alhamis, sun tasa keyar attajirin dan kasuwa.

Duk da ba a samu rashin rai ko daya ba, mazauna garin sun ce karamin yaro ya raunata bayan an bindige kunnensa.

Miyagun ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki jihar Kano kuma sun tasa keyar wani attajirin dan kasuwa dake karamar hukumar Dambatta a jihar.

‘Yan bindigan sun kai farmakin garin Kore a tsakar daren Alhamis inda suka dinga ruwan wuta babu sassauci, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wannan mummunan hari yana zuwa ne bayan kwana daya da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yayi korafin cewa miyagu sun fara tattaruwa a dajin Falgore dake jihar Kanon.

Kamar yadda muka sanar maku a baya cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci hukumomi da su yi hanzarin tarwatsa miyagun dake tattaruwa a dajikan Kano kafin al’amuransu su yi karfi.

Kamar yadda mazauna garin suka sanar, hantarsu ta kada sosai ganin masu harin sun shiga cikin gari a babura suna ruwan wuta, al’amarin da yasa mazauna yankin fadawa dajika cikin dare.

Sun sanar da cewa basu samu daukin jami’an tsaro ba koda aka kai farmakin, hakan yasa suka tasa keyar wani attajirin dan kasuwa a garin.

Mazauna garin sun sanar da cewa ba a yi asarar rai ko daya ba, sai dai wani karamin yaro ya samu rauni sakamakon harbin bindiga da ya taba kunnan shi.

Daga Ahmad Aminu Kado..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *