Yan Bindiga Na Bukatar Naira Miliyan Dari Da Goma kamin su sako daliban makarantar Islamiyya

Yan bindigan sun bukaci a biya su naira miliyan dari da goma kamin su sako daliban makarantar Salihu Tanko dake Tegina wadanda aka kwashe kwanaki da suka wuce.

Shugaban Malaman makarantar Abubakar Alhassan Gimi ne ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da Masu rahoto.

Abubakar wanda shima akwai yaransa biyu a cikin daliban ya Roki Gwamnati dama Al’umma da su taimake su wajen ganin an kubuto da daliban cikin koshin lafiya.

Yace sun zanta da Yan’Bindigan ne ta wayar daya daga cikin malaman dake hannun yan Bindigan.

Har dai yanzun yace babu takamemen adadi daliban da aka sacen.

Daga: Maryam Ango

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *