‘Yan Bindiga Sun Hana ‘Yan Kasuwa Komawa Garuruwan Su A Katsina.

Ajiya talata ‘yan Bindiga sun hana daruruwan ‘yan kasuwa komawa gidajensu bayan sun kammala hidindimun cin Kasuwar garin Kankara.

‘yan ta’adda dauke da bindigu sun tare hanyar data tashi daga garin Kankara Zuwa Kaikabayas,Malali,Pauwa,Zangon Zabaro,Makera, Dansabau harzuwa garin hayin Bedi dake cikin Jihar Zamfara ayau da misalin karfe 4:30.

Majiyar mu ta tabbatar mana cewa zuwa daren’yan kasuwar na jibge agefen hanyar dake bakin garin Kankara.

Azantawar da Wakilin Rana24 yayi da wasu daga cikin ‘yan Kasuwar da aka tare hanyar tasu sun bayyana sun tsayane domin labarin da suka samu cewar ‘yan ta’adda ne suka tare hanyar komawarsu gidajensu.

Hakazalika wani direba ya kara dacewa bayan ya kammala lodi ne yakama hanyarshine da komawa gida yayi cinkaro da shugaban tsaro na Karamar hukumar Kankara wato DPO cikin mota maisulke inda ya umurceshi Daya dawo Hanyar bata kyau inda nan take ya juya da motar shi zuwa dawowa cikin garin Kankara domin tsira da rayuwakansu.

Direban yakuma koka da irin tsananin Matsalar rashin tsaro da addabi yanki nasu. Bugu da Kari ‘yan Bindiga sun sha alwashin hana Noma awannan yanki daya shafi Kankara da wasu yankunan Faskari,Hayin Bedi, dake cikin Jihar Zamfara.

Daga Karshe al’ummar wannan yankin sunyi kira ga Gwamnatin data sanarda da isassun Jami’an tsaro da kuma Samar masu isassun Kayayyakin aiki da Kuma basu damar yin aikin tsaro.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *