‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyen Sakaba, Inda Suka Kashe DPO Da ‘Yan Sanda Uku Tare Da ‘Yan Sa Kai A Jihar Kebbi

Yan bindigan daji sun farmaki kauyukan karamar hukumar Sakaba na Jihar kebbi da safiyar Lahadi 25/4/2021, tare koran kimanin shanaye 1000, tare da tafka mumunan ta’asa a yankin.

‘Yan daban dajin, sun shiga yankin garin Makuku ne da misalin karfe 9 na safe, suka yi ta tattara shanun bayin Allah suna kora su.

Majiyarmu ta ce ana zargi, tare da fargabar cewa ‘yan daban dajin sun halaka babban jami’in yan sanda DPO na karamar hukumar Sakaba, tare da ‘yan sanda 3 da kuma wasu ‘yan sa kai.

Mun samo cewa jami’an tsaron sun fuskanci yan daban dajin ne bayan samun labarin farmakinsu, amma sai yan daban dajin suka yi masu kwanton bauna suka afka masu, lamari da ya haifar da mumunan zubar da jini tsakanin yan daban, da jami’an tsaro.

Kawo yanzu dai, babu wani tabbaci kan adadin mutane da suka mutu a wannan artabu tsakanin jami’an tsaro da Yan daban daji wanda har karfe 9:30 na dare ana fafatawa tun karfe 9 na safe da Yan daban dajin suka shiga yankin.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *