‘Yan Bindiga sun kashe mutun uku 3 tare da sace mutun takwas 8 a jihar Sokoto.

Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe mutane uku a kauyen Garin Zogo da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Sun kuma kori kauyuka takwas a karamar hukumar.
Da yake tabbatar da hare-haren wani da ke wakiltar yankunan, Ibrahim Muhammad Saraki ya ce an kaiwa Garin Zogo hari ne a ranar Juma’a da misalin karfe 10:30 na dare.

“Sun kashe mutane uku sannan suka ji wa daya rauni. Sun kuma yi awon gaba da dabbobi, sun kutsa cikin shaguna da yawa sun kwashe kayan da ba a san adadinsu ba, ”inji shi

A cewarsa, ‘yan fashin sun kuma kai hari kauyukan Nasarawa, Gidan Idi da Rambadawa a ranar Asabar inda suka raunata mutum uku da dabbobin da suka yi sata.

Ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun kara shiga gidajen mazauna yankin tare da kwace musu kayayyakinsu.

“Ba ma zama cikin kwanciyar hankali a cikin al’ummu saboda kisan na faruwa ne a kowace rana.

Kamar yadda nake magana da kai yanzu mutanenmu ba su daina kwana a gidajensu ba. Suna kwana a garin Sabon Birnin kuma suna dawowa da safe, har da ni.

“Kuma akwai wasu kauyukan da ba kowa ciki kamar Rambadawa, Garin Idi, Tudun Wada, Nasarawa, Tamindawa, Garin Ango, Tsaunar Dogo da Tashalawa,” in ji shi

Sai dai ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki.

Mashawarcin na musamman ga shugaban majalisar kan harkokin tsaro, Lamiru Umar yayin da yake tabbatar da hakan ya ce, a yanzu haka wasu mutanensu na samun mafaka a kauyen Tsululu da ke Jamhuriyar Nijar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Sakkwato, ASP Sunusi Abubakar ba a samu jin ta bakinsa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *