Yan sanda a jihar Nasarawa sun tabbatar da kisan shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, Alhaji Muhammad Husseini.
Mai magana da yawun jihar, ASP Ramhan Nansel a wata hira ta wayar tarho da Rediyon Najeriya a Lafia, ya ce an kashe Alhaji Muhammad a Kasuwar Gudi da ke karamar Hukumar Kokona a jihar.
Ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga biyu sun isa dandalin kasuwar da misalin karfe 7 na yamma a ranar Juma’a, sun kuma kashe Shugaban Karamar Hukumar Toto na MACBAN Alhaji Muhammad Umar.
An fara farautar maharan, ASP Nansel ya kara da cewa.