‘Yan bindiga sun sace daliban makarantar islamiya sama da 100 a Niger

Wasu yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a wata makarantar islamiya a garin Tegina jihar Niger.

Wani ganau ya tabbatar wa majiyar Katsina Daily Post News cewa, maharan sun kai hari ne a Islamiyar mai dauke da dalibai sama da 200

Akwai dalibai da yawa a lokacin da suka zo sama da 200, amma wasu sun rika tserewa ta taga.

“Tabbas akwai sama da dalibai 100 da aka sace, amma daga baya sun rika koro yaran da ba su fi shekaru 4 zuwa 12 ba domin sun yi kankanta da yawa,” in ji shugaban makarantar.

Ya kara da cewa da misalin yammacin ranar Lahadi ne ‘yan bindigar suka shiga garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi a jihar ta Neja.

“A babura suka isa wajen dauke da bindigogi, babu wanda ba a firgita ba a garin, tunda harbe-harbe kawai suke yi ta ko ina,” a cewarsa.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *