Yan Bindiga Sun Sace Mutun 15 A Karamar Hukumar Faskari A Jahar Katsina.

INNAH LILLAHI WA’INNA ILAIHIR
RAJI’UN😭😭😭

Wasu ‘yan bindiga sun shiga kauyen unguwar sani a gundumar mazabar ‘yan kara, inda sukai ta harbe harbe tare da yin garkuwa da mutun goma sha biyar 15 a karamar hukumar faskari dake jahar katsina.

A rahoton da muka samu yanzu ‘yan bindigar sun share kusan kimanin tsawon awa biyu suna barin wuta a garin, inda suka ci karensu ba babbaka har suka fice.

A cikin ‘yan kwanakin nan karamar hukumar Faskari na fama da hare haren ‘yan bindiga, domin babu ranar da zata fito ta koma ga Allah ace ‘yan ta’adda basu shigo yankin suka kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu don neman kudin fansa ba.

Ya kamata Gwamnatin jahar katsina data tarayya da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki dasu maida hankalinsu a wannan gari tare da sauran garuruwan dake fama da matsalar tsaro katsina da suyi duk mai yiyyuwa, domin daukar matakin da ya dace, don ganin an kawo karshen hare haren ‘yan bindiga a wadannan yankunan.

Alfarmar wannan wata na Ramadan muna rokon Allah ya kawo mana karshen wannan masifa ya kubutar da dukkan mutanen dake tsare a hannun wadannan azzaluman mutanen.

Daga Ahmad Aminu Kado…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *