‘Yan Gudun Hijira Sunyi Zanga-Zanga Sun Tare Babban Titin Makurdi Zuwa Lafia

Dururuwan mutanen da suke zaune a sansanin yan gudun hijira sun rufe babban titin Makurdi zuwa Lafia kan mutuwar wasu mutane 10 da ake ce makiyaya ne suka kashe a daren ranar Litinin a sansanin, The Nation ta ruwaito.

Sun tare babban titin tare da gawarwakin yan uwansu da aka kashe wanda hakan ya janyo cinkoson ababen hawa a babban titin.

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya tafi wurin da yan gudun hijiran ke zanga-zangar inda ya roke su da su bude hanyar domin motocci su rika wucewa.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *