Labarai

‘Yan gudun hijirar Najeriya a Chadi da Kamaru da Nijar yanzu sun kai 339,669 — MDD

Spread the love

Dangane da karuwar rashin tsaro a sassa daban-daban na kasar, wani rahoto da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa yanzu haka Najeriya tana da ‘yan gudun hijira 339,669 a kasashen Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Nijar.

Ministar jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban jama’a, Sadiya Farouq, a watan Satumba na shekarar 2021, ta ce adadin ya kai 322,000, wanda ya nuna karuwar kusan 17,000.

Sai dai, bisa ga bayanin da UNHCR ta buga kan ‘Yan gudun hijirar Najeriya ta hanyar mafaka a ranar 30 ga Nuwamba, 2022, adadin ‘yan Najeriya da ke neman mafaka a Jamhuriyar Nijar ya kai 187,130, da 132,151 a Kamaru da kuma 20,388 a Chadi.

Wannan mummunan yanayi bai rasa nasaba da kashe-kashe da sace-sacen jama’a a fadin kasar wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Wannan rahoto dai na zuwa ne duk da alkawarin da gwamnatin Najeriya ta yi na ba da muhimmanci ga gaggauta dawo da ‘yan Najeriya da rikicin ‘yan tada kayar baya a yankin Arewa maso Gabas ya raba da gidajensu daga kasashen Kamaru da Nijar da kuma Chadi a farkon watan Maris.

A watan Fabrairun wannan shekara ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin da shugaban kasa ya kafa na maido da ‘yan gudun hijira da kuma sake tsugunar da ‘yan gudun hijira.

Da yake jawabi a taron farko na kwamitin a watan Maris, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya sake nanata matakin gaggawar dawo da ‘yan Najeriya da ke gudun hijira a wasu kasashe.

“Ya kamata mu gaggauta yin duk abin da ya kamata don fara aikin dawo da mutanenmu gida. Tuni dai akwai tsare-tsare da dama,” in ji Osinbajo.

A cikin wani bugu na ranar 1 ga Disamba, 2022 mai taken “Nigeria: Populations At Risk”, Cibiyar Kula da Al’umma ta Duniya ta koka da karuwar mace-macen da ‘yan ta’adda ke yi a kasar.

Kungiyar ta ce yawan kashe-kashen da ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya ke shiryawa ya sa mutane da dama suka rasa matsugunansu a fadin kasar nan, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button