‘Yan Kungiyar kwankwasiyya kwakwalwar jakai ne dasu Kuma Kungiyar haukace ~Inji Ganduje.

A wani gajeran faifai mai dauke da sautin Murya an jiyo Gwamna Ganduje Yana Cewa Kungiyar kwankwasiyya asara ce
Kungiyar kwankwasiyya bala’ice
Kungiyar kwankwasiyya Haukane Kuma dakikai ne Domin kansu baya ja kwakwalwar su ta jakai ce inji Gwamna Ganduje.

A baya dai Gwamna Ganduje na daya daga cikin jiga jigai a tafiyar kwankwasiyya, ƙarƙashin jagorancin Sanata Eng. Dr. Alh. Rabi’u Musa Kwankwaso.

A shekarar 2015 ne Ƙungiyar ta kwankwasiyya ta tsayar da gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR. Khadimul Islam takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar APC, bayan karewar wa’adin mulkin Jagoran Ƙungiyar na kasa Eng. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso.

Bayan darewar Gwamna Ganduje kan karagar mulki ne sukai ta watse tsakaninsa da Kwankwaso, wanda hakan ne ma ya jawo fitar shi daga ƙungiyar kwankwasiyya tare da cire jar hula wadda ita ce alamar ‘yan kwankwasiyya.

Yanzu dai Abin jira a gani bai wuce martanin da Jagoran kwankwasiyyar Eng. Rabi’u Musa Kwankwaso zai mayar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *