‘Yan Nageriya sun kaiwa Buhari hari da muggan Kalamai Kan Rashin Zuwa Jana’izar Janar Attahiru.

‘Yan Nageriya da dama na Cigaba da Ruwan Kalamai Kan Rashin zuwan Shugaba Buhari Jana’izar Shugaban Sojojin Nageriya Janar Attahiru Ibrahim
Jama’a da dama sun zargi Shugaban da Rashin tausayi tare da Rashin martaba Kasa da tsaron ta
Ga dai Maganar tsohon na hannun damar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce abin takaici ne yadda shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya yi tattaki zuwa Paris kwanan nan amma ya gaza halartar jana’izar marigayi Shugaban hafsin sojan kasar nan Lt. Janar Ibrahim Attahiru, a Abuja ranar Asabar.

A shafin Jaridar Punch ta wallafa bayani game da Rashin zuwan Shugaban Jana’izar Lamarin da yasa jama’a Suka dunga tofa zage zage ga Shugaba Buhari ga dai Daya daga Cikin masu sharshin Mai suna Azez issah Ishola inda Yace Yakamata kawai
Buhari ya tura wakilai zuwa makabartar kamar irin su makaryata Lai Muhammad da sauransu…

Shi kuwa Wada Bako cewa yayi
Ba zai yiwu ba! Babban hafsan hafsoshin NIGERIA da sauran manyan janar-janar na soja sun Yi jihadi a aikin soja kuma shugaban kasarmu da ke da cikakkiyar lafiyar daya dawo daga Paris mai nisa ba zai iya dan tattaki ba don girmamawa ga jarumai ba Amma kash. Mugayen mashawarta ne a kusa da shugaban sun fi makiyan sa masu kishin kasa hatsari. Ba za mu iya kare wannan ba kuma. Ya bambanta da wanda na zaba sau biyu.

shima Kezzi Dominic Yace
Mun riga mun san dalilin dayasa bai halarci jana’izar ba … cewa shi ba buhari bane; zamu yada labarin idan ya halarta asiri zai tonu; gungun mahaukata kawai

Sai Kuma Devid Uyi yace
Zai fi aminci idan muka je Paris fiye da halartar wani taro a Abuja, idan wani ya yi tunanin wannan halin da muke ciki a yanzu Wanda muke da shi a Aso Rock yana tunanin wannan ƙasar a zuciyarsa to ya kamata a binciki Hankalin mutun.

Shima Shehu Muhammadu korau Yace
Balaguro zuwa ƙasashen waje yafi mahimmanci a gare shi; rashin tausayi da mugunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *