‘Yan Najeriya ne ke ta rokona in fito takarar shugabancin kasa, ~ Inji Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello yace dukkan ‘yan Najeriya ne ke ta rokonsa da ya fito takarar shugabancin kasa a 2023.

Gwamnan yace babu shakka akwai abinda mata da matasa suka hango a tare da shi ne, shiyasa suke ta wannan tururuwar garesa.

A cewarsa, kasar Najeriya tana bukatar tsayayyen mutum da zai iya hada kan jama’a, kuma babu shakka zai iya hakan.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *