Labarai

’Yan Najeriya nr ke da alhakin sauya tattalin arziki da siyasa – Buhari

Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su sauke nauyin da ya rataya a wuyan kasar wajen inganta tattalin arziki da siyasa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen rufe gasar karatun Alkur’ani ta kasa da aka gudanar a Gusau ranar Asabar.

Mista Buhari, wanda Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital, Isah Ali Pantami ya wakilta, ya ce ‘yan kasa ne ke da alhakin kawo sauye-sauye a matsalolin zamantakewa da tattalin arziki da siyasa na kasa.

Duk da cewa shugabanni suna da rawar da za su taka fiye da sauran mutane, Mista Buhari ya ce kowane dan Najeriya na bukatar ya yi aiki daidai domin samun al’umma ta gari.

Shugaban ya kuma yi kira ga shugabanni a dukkan matakai da su rika nuna adalci da gaskiya da kyautatawa yayin da suke mu’amala da al’ummarsu, yayin da mabiyan su rika mutunta shugabanni da kuma kasancewa masu bin doka da oda.

Ya kara da cewa, idan mabiya suka mutunta doka za a samu Najeriya mafi inganci.

Daga nan sai ya yabawa Majalisar Sarkin Musulmi da Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato bisa gabatarwa da kuma ci gaba da gudanar da gasar karatun Alkur’ani a fadin tarayyar kasar nan tsawon shekaru 37.

Sannan ya kuma yabawa gwamnatin Zamfara da al’ummar jihar bisa yadda suka karbi bakuncin mahalarta gasar.

Shi ma a nasa jawabin, Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya ce Majalisar Sarkin Musulmi za ta hada kai da Jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sakkwato, domin ganin dubban masu karatu sun zurfafa bincike da nazarin Alkur’ani.

Sarkin Musulmi ya kara da cewa ya kamata su kara zurfafa tunani kan karatun Alkur’ani a matsayin hanyar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya godewa kwamitin Musabaka na kasa bisa baiwa jihar damar karbar bakuncin taron karo na 37.

Ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen yadawa da inganta koyarwar addinin musulunci ta hanyar kafa cibiyoyin shari’a guda 11 a jihar.

Nura Abdullahi na Sokoto ne ya zama gwarzon shekara a masarautar Sarkin Musulmi, yayin da Aishatu Abdulmutallib ta Yobe ta lashe ajin mata kuma matar gwamna Matawalle, Aisha ta ba ta kyautar gwarzon shekara.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button